fbpx
Monday, March 1
Shadow

Gwamnatin Tarayya Za Ta Dauki matasa 30,960 aikin tsaro na musamman a Fadin Najeriya

Gwamnatin Tarayya za ta dauki wadanda suka kammala karatu 30,960 a matsayin jami’an tsaro na  na shirin kare al’umma don manufar Tsaron Dan Adam (CSHSP) a Najeriya.
Kowace daga cikin kananan hukumomi 774 a kasar za ta samu jami’ai 40.
Da yake kaddamar da wani kwamiti na mutum 17 a kan CSHSP a Abuja a ranar Litinin, Ministan Ayyuka na Musamman, George Akume, ya ce wannan don tsara dabarun yadda za a rage aikata laifuka da tashin hankali a kasar.
“Wannan shi ne don samun bayyanai game da lafiyar al’umma, na farko a matakin gida wanda a mafi yawan lokuta yake zama madogara ga dukkanin manyan tashe-tashen hankula da rikice-rikicen da suka rikide zuwa matsalar kasa.”
Akume, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya ce an kuma tsara shirin ne domin samar da ayyukan yi sama da dubu 30 ga matasa da kuma samar da kwararrun ma’aikata mata sama da dubu 50 a duk fadin Nijeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *