fbpx
Friday, July 1
Shadow

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kirkiro Ayyukan Yi Miliyan Biyar>>Ministan Masana’antu da Sana’oi, Otunba Richard Adeniyi Adebayo

Ministan Masana’antu da Sana’oi, Otunba Richard Adeniyi Adebayo, ya ce tsarin farko na farfado da tattalin arzikin da Gwamnatin Tarayya za ta gudanar zai samar da ayyuka tare da hana ayyuka miliyan biyar durkushewa.

Gwamnatin tarayya ta bijiro da tsarin ne domin magance tabarbarewar tattalin arzikin kasa ne sakamakon annobar cutar korona.
Ministan ya ce akwai tsari a kasa da zai hana durkushewar akalla ayyukan yan Najeriya miliyan daya da dubu dari hudu, wanda kashi 40 kananan sana’oin mata ne da nakasassu.
Adebayo ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda da Mai taimaka masa a harkokin yada labarai, Julius Toba-Jegede, ya sanya wa hannu ranar alhamis.
Ministan ya kara da cewar wannan wani yunkuri ne da ma’aikatarsa ke yi na ganin an yi nasara a shirin gwamnatin tarayya na farfado da tattalin arzikin a wannan yanayin da duniya take ciki na annoba.
Ya ce, domin samun nasara akan hakan, sun bijiro da shiri guda uku kamar haka:
Asusun da zai tallafa wa masu matsakaita da kuma kananan sana’oi.
Shirin da zai bayar da tallafai ga masu son fara sana’oi.
Sai kuma tsarin bayar da rance ga matsakaita da kuma kananan sana’oi don su tsaya da kafafunsu.
Ya ce, shiri zai samar da ayyuka miliyan biyar, ya taimaka wa masana’antu wajen gudanarwa da kare su daga durkushewa da kuma habbaka sana’oin masana’antun, tare kuma da hana su jin radadin annobar ta cutar korona.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Gwamna Wike zai ganada Bola Ahmad Tinubu a kasar Faransa

Leave a Reply

Your email address will not be published.