Gwamnatin tarayya ta shirya tsaf dan Aro kudi daga Banki Dutch da na kasar Brazil dan inganta harkar noma.
Me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar Noma na musamman, Andrew Kwasari ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai a jiya, Laraba.
Yace wannan na karkashin tsarin gwamnati na harkar Noma wanda a kowace karamar hukuma zaa samar da Ofishin da zai rika kula da harkar Noman kuma ‘yan kasuwane zasu kula da wadannan cibiyoyi.
Yace kuma ‘yan kasuwar ne dai za’a baiwa bashin da za’a ciyo kuma sune zasu biyashi.