fbpx
Monday, August 15
Shadow

Gwamnatin tarayya zata dakatar da DailyTrust da BBC kan labaran da suke wallafawa na ‘yan bindiga

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata dakatar da kamfanonin manema labarai na DailyTrust da BBC kan labaran da suke wallafawa na ‘yan bindiga.

Sau da yawa manema labaran suna wallafa labarai kan ‘yan bindiga wanda gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa hakan na sake jefa kasar cikin mawuyacin hali.

Ministan labarai da kuma kabilu, Lai Muhammad ne ya bayyana hakan yayin dayake ganawa da manema labarai ranar alhamis.

Inda yace labaran nasu na karawa ‘yan bindigar karfi suna samun damar cigaba da ta’addancin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.