fbpx
Monday, August 15
Shadow

Gwamnatin tarayya zata ginawa tsohon shugaban alkalai Tanko katafaren gida tara da naira biliyan 2.5 duk da cewa ana zarginsa da satar kudin kasa

Gwamnatin tarayya zata ba tsohon shugaban alkalai da yayi murabus ranar litinin, Ibrahim Tanko Muhammad naira biliyan 2.5 duk da ana zarginsa da satar kudi a mulkin nasa.

Manyan alkalan Najeriya guda 14 sun zargi tsohon shugaban nasu da satar kudi kuma tun kafin yayi murabus sun bukaci a tsige shi ko su daina aiki.

Kuma shugaba Buhari ya rantsar da Olukayode Ariwoola a matsayin shugaban alkalan na wucin gadi.

Gwamnatin tarayya zata ginawa Tanko katafaren gida a babban birnin tarayya ko kuma a kowace jihar da yeke so sannan kuma zata bashi naira biliyan 2.5 a matsayinsa na tsohon shugaban alkalai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.