Gwamnatin tarayya zata kashe Jimullar Naira Biliyan 3.3 akan tsaffin shuwagabannin da suka ajiye aiki da manyan jami’an gwamnati.
Tsaffin manyan ma’aikatan gwamnati zasu samu jimullar Naira Biliyan 1 da za’a raba musu. Sai kuma tsaffin shuwagabannin kasa da mataimakansu da za’a rabawa Naira Biliyan 2.3.
Wannan bayani na kunshene a cikin kasafin kudin da majalisar tarayya ta amince dashi na shekarar 2023.