fbpx
Friday, February 26
Shadow

Gwamnatin Tarayya Zata Samar da Kamfanin Sarrafa Shinkafa 3 da Taraktoci a Jihar Adamawa

Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Bunkasa Kasa ta Noma (NALDA), ta shirya tura injinan casarar shinkafa uku a Jihar Adamawa a matsayin wani bangare na matakan bunkasa noman cikin gida, da kara daraja da kuma bunkasa kudaden shigar manoma.
Htuduole ya ruwaito muku cewa, Sakataren zartarwa na NALDA, Prince Paul Ikonne, ya fadawa manema labarai a Abuja ranar Lahadi cewa wannan shi ne sakamakon tattaunawar da ya yi da manoma a jihar.
Ikonne ya ce hukumar ta gano gonakin NALDA da ake da shi, kimanin hekta 4,000, kuma ta samu karin gudummawar filaye.
Ya ce hukumar ta kuma samu karin hekta 5000 a ziyarar da ta kai Fulfulde a jihar.
A cewarsa, kamfanonin shinkafar sun zama dole saboda jihar na samar da shinkafar da ba a sharrafa ba mai yawa da ke fita don sarrafa shi a wani wuri.
Ya ce: “NALDA na kawo injinan sarrafawa wadanda za su kasance a wurare daban-daban guda uku domin sarrafawa da kuma ba wa amfaninsu muhimmanci.
Shugaban na NALDA ya ce ya kasance a jihar ta Adamawa ne biyo bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na zuwa farfado da dukkan filayen NALDA dake al’ummomin da bunkasa su da kuma samarwa da mutane arziki.
Don cimma wannan, ya ce NALDA za ta bai wa manoma ingantaccen iri, su ba da sabis na faɗaɗawa da taraktoci; “Yayin da hukumar ke sayan girbin a farashi mai tsoka don kauce wa cinikin manoma ta ‘yan tsakiya.”
Dangane da biyan diyya ga taraktocin, ya ce: “Ba za ku biya kudi a ciki ba, amma lokacin da muke sayen kayayyakin da kuka girbe, za mu rage wani kaso na kudin bisa lamuran taraktar da kuka yi amfani da su ta yadda za mu iya ci gaba da amfani da taraktan. ”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *