fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Gwamnatin Zamfara ta Kubutar da mutane 10 daga hannun masu garkuwa da mutane

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sake tabbatar da sakin mutane goma da aka sace ba tare da biyan kudin fansa ba.
Wadanda aka sacen sun kwashe sama da watanni uku da makonni biyu sun ce an sace su ne a yankin Gwaram da ke karamar hukumar Talata Mafara ta jihar.
Daga cikinsu akwai maza uku, ciki har da mahaifin daya daga cikin ‘Yan matan Makarantar Jangebe da aka sace, mata hudu da yara uku.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar, Abubakar Dauran, ya ce an kubutar da su ba tare da kudin fansa ba ta hanyar shirin zaman lafiya na gwamnatinsa.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tattaunawar zaman lafiya, yana mai cewa hakan hanya ce da za ta samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar.
“Muna shaida wata nasarar da aka samu ta fuskar tsaro inda aka ceto mutane goma, wadanda aka yi garkuwa da su a Gwaram a karamar hukumar Talata-Mafara wanda a cikinsu daga cikinsu mahaifin dalibar makarantar Jangebe,” in ji shi.
“Na yi imanin idan ba tattaunawa muke yi ba a Jihar Zamfara, ba shakka ba za mu iya ceton waɗannan mutane ba. Har yanzu muna tare da wannan tattaunawar kuma tare da nuna rashin son kai, dole ne mu ci gaba da yi saboda halin da muke ciki a jihar Zamfara, mun san yana da mahimmanci amma muna samun nasarori da yawa.
“Kwanan nan, mun kubutar da ‘yan matan makarantar Jangebe 279, kafin haka mun gano kimanin makamai 20 daga dan Buharin Daji wanda ya mika kansa bisa son rai tare da wasu harsashi mai rai na daban.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

Leave a Reply

Your email address will not be published.