fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Gwamnatin Zamfara ta saka dokar hana zirga-zirga a Jangebe, Ta kuma Zargi me gadin makarantar da hannu wajan satar Dalibai

Gwamnatin jihar Zamfara ta saka dokar hana zirga-zirga a garin Jangebe na karamar hukumar Talatar Mafara saboda rikicin da aka samu.

 

Hakan na zuwane bayan sakin dalibai mata na makarantar garin su 279. Kwamishinan yada labarai, Hon. Sulaiman Tunau Anka ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

 

Yace dokar zata tabbatar an dawo da zama lafiya a garin, wasu Rahotanni dai sun bayyana cewa jama’ar garin sun rika jifar jami’an tsaro da sukawa ‘yan matan da aka sace rakiya wanda ya kawo hatsaniya

 

“Similarly, there is strong discovered evidence of market activities in the town that aid and abet bandits’ activities in the town and neighboring communities.

“Consequently, all market activities in the town are hereby suspended until further notice,” he said.

 

A wani Labarin me kama da wannan kuma Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa ‘yan matan da aka sako sun bayyana cewa ‘yan Bindigar sun gaya musu cewa me gadin makarantarsu ne ya taimaka musu wajan sacesu.

Karanta wannan  Yadda hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad ya cigaba da karbar albashin miliyoyin naira duk da yayi murabus

 

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channelstv inda yace ‘yan Bindigar har sun baiwa yaran sakon su gaishe da me gadin inda har kiran sunansa suka yi.

 

Gwamnan ya bada tabbacin cewa za’a yi bincike dan gano gaskiyar Lamarin.

 

“The children have mentioned the watchman of the school, that after releasing them, the bandits were telling them that they should greet the watchman for them, they even mentioned his name that he was the one who gave them the go-ahead to come, he was involved.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.