Gwamnonin Arewa 9 sun bayyana cewa dan kudu suke son a baiwa takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
A mako me zuwane dai APC zata tsayar da dan takarar da zai nemi shugaban kasa a karkashinta.
Saidai wasu na ganin tunda PDP ta tsayar da Atiku, kamata yayi a tsayar da dan Arewa a jam’iyyar APC dan tafiyar ta yi daidai.
Gwamnonin Zamfara, Kwara, Naija, Katsina, Kano, Kaduna, Filato, Borno, duk sunce dan kudu suke son a tsayar takarar shugaban kasa a APC din.