A ranar alhamis gwamnoni da ministoci tare da shugawgabannin APC na arewa masu yammacin kasar nan suka gudanar da taro a babban birnin tarayya Abuja.
Inda suka bayyana cewa a yankin su ya kamata Bola Ahmad ya zabi abokin takararsa domin sun fi ko’ina yawan kuru’u a Najeriya.
Duk da cewa dai APC ta bayyana tsohon maji dadinta Kabiru Masari a matsayin abokin takarar Tinubu, rahotanni sun bayyana cewa ta gabatarwa da INEC shi ne saboda kar ta wuce wa’adin da hukumar zaben ta bayar.
Amma APC ta zabi Masari ne na wucin gadi kafin ta bayyana na asalin da zata zaba, kuma da yiyuwar a kudu masu yammacin kasar nan zata zabarwa Tinubu abokin takara.