Saturday, November 2
Shadow

Gwamnoni sun kashe Naira Biliyan dari tara da sittin da takwas(968,000,000) wajan Shan kayan zaki da Alawus din taruka a watanni 3 da suka gabata

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Najeriya 30 sun kashe Naira biliyan dari tara da sittin da takwas, N986.64bn wajan shan kayan ruwa da alawus din taruka da tafiye-tafiye da sauransu.

Watau dai wadannan kudade ba’a kashesu kai tsaye wajan yin wani aiki da zai amfani al’uma ba.

An samo wadannan bayanai ne daga kundin tattara bayanan yanda gwamnati ke kashe kudaden kasa saidai babu bayanan jihohi 6, Benue, Imo, Niger, Rivers, Sokoto da kuma jihar Yobe.

Bayanan sun nuna cewa jihohi 3 din sun kashe Naira Biliyan 5.1 wajan baiwa baki kayan ruwa watau lemu da ruwan sha da sauran kayan zaki.

Karanta Wannan  Na cika duk Alkawuran dana daukarwa 'yan Najeriya>>Shugaba Tinubu

Sannan sun kashe Naira Biliyan 4.67 a matsayin Alawus ga ma’aikatan gwamnati.

Jihohin sun kuma kashe Naira Biliyan 34.63 wajan tafiye-tafiye a cikin gida da kasashen waje hakanan kuma sun kashe Naira Biliyan 5.64 wajan biyan kudin wuta dana ruwa da sauransu.

Jihohin sun kuma kashe Naira Biliyan dari hudu da biyar, N405.77bn wajan biyan ma’aikatan jihohinsu Albashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *