fbpx
Monday, June 27
Shadow

Gwamnonin APC na kokarin samar da dan takarar shugaban kasa na bai daya amma abu ya ci tura

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin jam’iyyar APC na ta ganawa dan samar da dan takarar shugaban kasa na bai daya kamar yanda shugaba Buhari ya bayar da umarni amma abin ya faskara.

 

Wata majiya daga wajan taron ce ta sanar da jaridar Punchng haka inda tace an daga taron zuwa wata rana a nan gaba cikin makon da muke.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari dai ya baiwa gwamnonin aikin samar da dan takara guda daya wanda yace ba sai an yi zaben fidda gwani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.