fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Gwamnonin APC sun yiwa Tinubu Alkawarin zai samu nasara a jihohi 22 da suke mulki

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya bayyana cewa, Gwamnonin APC sun yiwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmad Tinubu alkawarin lashe zabe a jihohi 22 da suke mulki.

 

Ya bayyana cewa, gwamnonin zasu kawowa Tinubu wadannan kuri’u ne saboda irin ayyukan ci gaba da sukaiwa jama’ar su.

 

Ya bayyana hakane a Daura bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

 

Gwamna Hope Uzodinma da takwarorinsa sauran gwamnoni sun jewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari gaisuwar Sallah a Daura.

Karanta wannan  Gwamnonin Najeriya na shan suka kan shawarar da suka baiwa shugaba Buhari ya sallami ma'aikatan da suka kere shekaru hamsin

 

Akan maganar zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin Bola Tinubu, Hope Uzodinma yace abune wanda dukansu sun amince dashi kuma suna farin ciki da hakan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.