fbpx
Friday, February 26
Shadow

Gwamnonin Arewa da ke goyon bayan a tsayar da dan kudu takarar shugaban kasa a 2023

A yayin da saura watanni 27 wa’adin Mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kare, anata cece-kuce da muhawara kan wamda za’a sayar takarar shugaban kasa a zaben 2023 a jam’iyyar APC.

 

Hakanan itama jam’iyyar PDP ta fara harama inda ake ta yawo da labarai kala-kala akan dan takarar da zata tsayar.

 

Saidai kasancewar shugaban kasa, Muhammadu Buhari dan Arewane, ana tsammanin dan kudu ne za’a tsayar takarar shugaban kasa a 2023, duk da hakan ba yana cikin kundin tsarin mulki bane.

 

Tuni dai wasu manyan ‘yan siyasa daga Arewa suka bayyana goyon bayan cewa kudu ya kamata ta yi mulki a 2023.

 

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai:

 

Gwamnan Kaduna na daga cikin wanda ke ganin kamata yayi ace dan Kudu ne zai yi shugabanci a shekarar 2023.

 

El-Rufai a lokuta daban-daban ya bayyana haka. A wata hira da aka yi dashi a BBC ya bayyana cewa ya kamata a bi tsarin karba-karba yanda idan shugaba Buhari ya gama to dan kudu ne zai karba.

 

In Nigerian politics, there is a system of rotation, in which everyone agrees that if the North rules for eight years, the South will rule for eight years.

“That is why I came out and said that after President Buhari has been in office for eight years, no northerner should run for the office. Let the southerners also have eight years.”

 

Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

 

Shima Gwamna Ganduje ya bayyana cewa kamata yayi ace dan Kudu ne zai tsaya shugaban kasa a shekarar 2023.

 

A wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channelstv,  gwamnan ya bayyana cewa, duk da babu tsarin a kundin tsarin mulkin Najeriya amma kamata yayi a tsayar da dan kudu a 2023.

 

“It should go to the southern part of the country, but there should be a consensus of members. The zoning system, even though it is not in the constitution of the Federal Republic of Nigeria, is a strategy for winning elections,” he said.

 

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum.

 

Shima Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum na daga cikin masu ra’ayin a tsayar da dan kudu takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

 

A wajan tunawa da Gani Fawehinmi a Legas, Gwamna Zulum yace dan hadin kan Najeriya ya kamata a barwa dan kudu yayi takarar shugaban kasa a 2023.

 

“The constitutional history of Nigeria’s dysfunction: Any pathway to indivisibility and common progress?” the governor said the country was moving into an inevitable tension.

 

“My response to the question posed by the theme of this programme is that, yes, there are pathways to indivisibility and common progress. We must collectively agree that we need to do more to demonstrate fairness to every constituent part that made up this country. That is the constitution.

 

Sauran wanda suka nemi a tsayar da dan takara daga kudu a Arewa sune, tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, Sanata Ali Ndume, Sanata Baba Kaita.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *