Wasu gwamnoni daga Arewa sun je jihar Oyo inda suka gana da Gwamna Seyi Makinde a sirrance.
Ganawar kokari ne na ganin an samar da zaman Lafiya da kwantar da hankula bayan rikin Yarbawa da Hausawa a Sasa dake jihar.
Gwamnonin Zamfara, Bello Matawalle, Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Naija, Abubakar Bello da Kebbi, Abubakar Bagudu. Channelstv tace zuwa yanzu dai babu cikakken bayanin abinda aka tattauna a zaman.