fbpx
Friday, July 1
Shadow

Gwamnonin Arewa sun mayar da harkar ‘yan bindiga kasuwanci>>Shugaban kungiyar matasan Arewa

Kungiyar matasan Arewa ta bakin shugabanta, Shattima Yarima ta bayyana cewa gwamnonin Arewar sun mayar da harkar tsaro kasuwanci.

 

Ya kuma zargi shugaba Buhari da rashin yin abinda ya dace wanda yace hakan yasa hare-haren sun kara kazanta a yankin na Arewa.

Yarima ya bayyana hakane a ganawar da yayi da Sahara Reporters inda ya bayyana cewa duk matsalar shugabanci ce ta jawo haka.

 

Ya zargi gwanonin da halin ko in kula kan harkar tsaro saboda kudin da ake warewa na musamman ga jihohin dake fama da matsalar tsaro wabda ba’a bincikensu ya jawo hanklin shugaba Buhari da cewa ya magance matsalar tsaron Katsina idan ba haka ba zata iya tsallakawa zuwa wasu jihohi makwabta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.