fbpx
Monday, March 1
Shadow

Gwamnonin Kudu maso Yamma ne ke da alhakin kashe-kashe a Ibadan – Sanata Ahmad Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, Asabar. ya caccaki Gwamnonin Kudu maso Yamma, yana zargin su da cewa su ne suka shirya kashe-kashen a Kasuwar Sasha da ke Ibadan, Jihar Oyo.

A cewar Lawan, gwamnonin ma suna da alhakin tashin hankali da hare-hare kan ‘yan Arewa a yankin Kudu maso Yamma.

A wata hira da manema labarai, Lawan ya danganta tashin hankalin yunkurin da aka yi na korar Fulani makiyaya daga jihohin Kudu maso Yamma, ya kara da cewa kalaman da wasu Gwamnonin Kudu maso Yamma suka yi ne ke da alhakin kashe-kashen a Kasuwar Sasha da ke Ibadan, Jihar Oyo da sauran hare-hare da aka kawai yan Arewa a yankunan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *