Gwamnonin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
Gwamnonin sun bayyana goyon bayanne a karkashin kungiyarsu ta NGF ta bakin shugaban kungiyar,Gwamna jihar Ekiti, Kayode Fayemi.
Sun bayyana cewa, suna farin ciki da nadin Gambari kuma a matakin jihohi zasu bashi goyon bayan daya kamata dan kaiwa ga nasara.