fbpx
Friday, July 1
Shadow

Gwamnonin Najeriya za su ɗaukaka ƙara kan ƙayyade kashe kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce za ta ɗaukaka ƙara game da hukuncin wata babbar kotu da ya kori ƙarar da suka shiga suna ƙalubalantar matakin da sashen tattara bayanan sirri kan hada-hadar kuɗi na ƙayyaɗe kuɗaɗen da ƙananan hukumomi za su rika kashewa a kullum.

Babbar kotun ta ce gwamnonin ba su da hurumin hana kayyade naira dubu 500,000 a matsayin kuɗaɗen da ƙananan hukumomi za su rika kashewa a kullum ba.

Abdulrazak Bello Barkindo daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar ya ce duk da cewa taron da gwamnonin suka shirya ranar Laraba bai yiwu ba, amma an cimma matsayar ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun.

Leave a Reply

Your email address will not be published.