Jam’iyyar PDP dai na ci gaba da samun rarrabuwar kawuna a kan layukan Arewa/Kudu, dangane da batun tikitin takarar shugaban kasa.
A jiya ne dai shugabannin jam’iyyar na Kudu maso Kudu da suka hada da gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya da tsaffin gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki suka bukaci a ba wa yankin tikitin tsayawa takara a bisa gaskiya da adalci.
Sai dai jam’iyyar ta bakin sakataren yada labaranta, Debo Ologunagba, ta bayyana cewa ba za ta hana yan yankin Arewa da suka nuna sha’awarsu ta tikitin tsayawa takara ba.
A taron da aka yi jiya a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, shugabannin yankin Kudu maso Kudu sun yi gargadin cewa jam’iyyar na iya rasa damar sake karbar ragamar mulki idan har ta kasa tsaida Dan yankin a matsayin dan dan takara.