An yi ta kwarzanta wani ɗan Najeriya saboda sayar da rayuwarsa da ya yi ya tuƙa wata tankar fetur da ta kama da wuta a ƙoƙarinsa na fitar da ita daga wajen da mutane suke don kar a yi ɓarna a birnin Warri na jihar Delta.
Ejiro Otarigho ya shai da wa BBC cewa “Abu ɗaya ne ya zo raina shi ne in tuƙa tankar mai cin wuta har zuwa wajen kogi mafi kusa.
“Mataimakina ne ya ankarar da ni cewa tankar tamu ta kama da wuta. Kuma wuta ce ganga-ganga ta kama,” a cewarsa.
Mista Ejiro ya sauke wani lodi kenan daga tankar tasa sannan ya kama hanyar zuwa wani wajen sai abin ya faru.
Ba tare da ɓata lokaci ba, ya shaida wa mataimakin nasa ya sauka daga motar inda shi kuma ya ƙara mata wuta don ficewa daga cikin mutane don gudun jawo ɓarna.
A wannan yanayin, duk wani dan kukure daga Mista Otarigho ko kuma a sau wata fashewa, da za su iya jawo mummunan bala’i.
“Niyyata ita ce na tuƙa motar har zuwa wajen kogi. Amma da na isa can sai sitiyarin motar ya cije sai na kasa ci gaba da tuƙawa,” ya faɗa.
“Na ce idan na tuƙa kai tsaye, motar na iya faɗuwa kuma za ta iya ƙara jawo matsala. Don haka dole na tsaya a wani buɗaɗɗen waje.”
A ƙarshe Mr Otarighoya samu nasarar kawar da tankar daga cikin mutane, kuma a wani bidiyo da ya yaɗu an ga yadda muatne suka baibaye shi suna murna.
Mr Otarigho ya tsira lafiya ba abin da ya same shi sai hayaƙi da ya shaƙa da kuma ƴan raunuka da ji a jikinsa.