fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Gwmnatin Buhari ta roki kungiyoyi masu zaman kansu su taimaka mata a magance matsalar tsaro

Gwamnatin shugaba Buhari ta roki kungiyoyi masu zaman kansu dake Najeriya su taimaka mata a magance matsalar tsaro ta ‘yan Bindiga.

Karamin ministan kasafin kudi, Clement Agba ne ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja jiya ranar talata yayin da ake kaddamar da wata kungiya mai zaman kanta ta SURE4U.

Tsohon jami’in dake lura da shige da fice na kasa ne ya hada wannan kungiyar, wato janar Muhammad Babandede domin taimakawa ‘yan kasa da kuma kare hakkin bil’adama.

Inda ministan ya nemi kungiyar ta saka hannu a cikin harkar matsalar tsaron da kasar Najeriya ke fama dashi domin a kawo karshen ‘yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published.