fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Gwmnatin jihar Niger zata hana karuwanci saboda magance matsalar tsaro

Gwamnatin jihar Niger ta bayyana cewa zata dakatar da karuwanci a fadin jihar domin kawo magance matsalar tsaro.

Sakatariyar ma’aikar mata ta jihar, Kaltun Rufa’i ce ta bayyana hakan yayin datake ganawa da manema labarai ranar talata.

Inda tace gwanatin bata da masaniya akan cewa al’ummar jihar na harkar karuwanci, wanda hakan ke kara kawo matsalar tsaro a jihar.

Saboda haka tace gwamnatin zata yi iya bakin kokarinta domin ta dakatar da harkar karuwanci a jihar, kuma dama can akwai hukunci mai tsanani akan masu aikata wannan bannar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.