Aloe Vera na gyara fatar fuska sosai inda yake kawar da dattin fuska da kara mata haske kuma idan aka duba za’a ganshi a cikin mayukan gyaran fuska da yawa.
Ga jawabin amfanin da Aloe Vera ke yiwa fata da kuma yanda za’a sarrafashi a samu abinda ake so.
Aloe Vera yana maganin duhun fata.
Yana magamin canjawar fuska da zafin rana ke kawowa.
Yana kawar da fatar data mutu a fuska wadda ke kawo duhun fuska.
Yana maganin ciwo a fuska.
Yana maganin kumburin fuska.
Yana maganin cizon kwaro irinsu sauri kudin cizo da sauransu.
Idan za’a sayi man shafawa dage dauke da Aloe vera a duba a tabbatar ba’a hadashi da giya ba ko sauran sinadarai masu kawowa fata illa.
Babbar hanyar samun amfanin Aloe vera a fuska, shine mutum ya hada kayansa a gida.
Yanda ake hada man Aloe Vera a gida:
Za’a yanko Aloe Vera da wuka daga jikin iccensa:
Sai a wanke a bari ya bushe.
Sai a sa wuka a yanke koren jikin Aloe Vera din.
Ana iya amfani da wuka a rika karto man dake jikinsa.
Ko a sa a wani abu a matso.
Idan aka samu ruwan, kada a hada da komai a zuba a mazubi a ajiye.
Domin ajiya me kyau, a ajiye a cikin firjin.
Kamin a shafa a fuska, a fara shafawa a hannu a barshi ya dade kamin a ga idan ya nuna alamar kaikai ko canjawar kalar fata ko kuma wani reaction na daban, kada a shafa a fuska saboda kada ya lalata fuskar, idan kuma bai nuna alamar komai ba, sai a shafa a fuskan.
[…] Ana samun ganyen Aloe Vera a kankare koren ganyen dake jikinshi a matso ruwan a rika shafawa a fuska dan maganin tabon fuska, mun yi cikakken bayani kan yanda ake amfani da Aloe Vera wajan gyaran fuska […]
[…] Hanya ta gaba itace ta amfani da Aloe Vera: […]
[…] kuma bata yi ba, sai a ci gaba har fuska ta dawo daidai. Ana iya karanta karin bayani kan amfanin Aloe vera wanda muka […]