Wani bincike ya tabbatar da ana amfani da madara a matsayin Cleanser a fuska dan kawar da kurajen fuska, duhun fuska, da matacciyar fatar fuska.
Binciken ya bayyana cewa, madarar tana kuma hana bakaken abubuwa bayyana a fuska da kuma bude kofofin gashin fuska.
Ana iya amfani da auduga ko kyalle me kyau a goga madarar a fuska.
Ana amfani da madara wajan kara hasken fata, kuma akwai mayukan kara hasken fata da yawa da aka hadasu da madara.
Saidai babu wani bincike na bangaren masana lafiya daya tabbatar da madara na kara hasken fata. Hakan na nufin za’a iya gwadawa a gani, idan yayi reaction sai a daina, idan kuma bai yi ba, za’a iya yin sati 4 ana gwadawa ana idan fata zata yi haske.
Bayan dadewa a rana, ana iya amfani da Madara a shafa a fuska dan kawar da duhun fuska da rana ke sawa.
Saidai wasu yana musu reaction, idan an ga reaction a daina, idan ba’a gani ba, za’a iya ci gaba da amfani dashi.
[…] Madara na daya daga cikin abubuwan da ake amfani dasu wajan kawar da pimples da black spot a fuska. A samu madara ko kyalle me kyau a yi amfani dashi wajan shafa madarar a fuska bayan an kwaba da ruwa. Akwai cikakken bayanin amfanin Madara wajan gyaran fuska da muka yi. […]