fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Haaland ba zai buga wasan Dortmund ba ranar lahadi yayin da Dahoud ba zai sake buga wasa ba a kakar bana

Erling Braut Haaland ba zai samu damar hallatar wasan Dortmund ba wanda zasu buga ranar lahadi tsakanin da Paderburn yayin da shi kuma abokin aikin shi Mahmoud Dahoud ba zai kara buga wasa ba a wannan kakar wasan.

Haaland da abokin aikin shi Mahmoud Dahoud sun samu raunika a ranar talata yayin da suke Karawa da kungiyar zakarun Bundlesliga Bayern Munich.
Haaland ya kasance daya daga cikin zakarun matasan yan wasan yayin da yaci kwallaye sama da 40 a wannan kakar wasan.
A ranar juma’a babban kochin kungiyar Dortmund Lucien Favre ya bayyana cewa Mahmoud Dahoud ba zai cigaba da buga wasannin wannan kakar wasan ba yayin da shima Erling Braut Haaland ba zai samu damar hallatar wasan ba a ranar lahadi. Sun fahimci hakan ne bayan sun buga wasa tsakanin su da Bayern.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Elon Musk zai saya kungiyar Manchester United

Leave a Reply

Your email address will not be published.