fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Haaland ya shirya barin gasar Bundlesliga>>Lothar Mathaus

Zakaran kasar Jamus Lothar Mathaus ya bayyana cewa tauraron dan wasan Dortmund ya shirya barin gasar Bundlesliga gami da neman shi na kungiyoyin zakarun gasar Premier League suke yi, wato Manchester United da kuma Mancheater City.

Haaland ya cigaba da kokari sosai a wannan kakar kamar yadda yayi a kakar bara, yayin da yayi nasarar cin kwallaye 17 a wasanni 14 daya buga. Manema labari na Sportmail ne suka bayyana cewa Manchester City da kuma United suna harin dan wasan mai shekaru 20.

Karanta wannan  Cristiano Ronaldo na son barin Manchester United ne saboda Lionel Messi, karanta kaji dalili

Kwantirakin Halland a Dortmund ba zai kare ba har sai nan da shekarar 2022 yayin da kuma yake da farashin yuro miliyan 65 a kwantirakin nashi, kuma Dortmund zata hanzarta siyar da dan wasan akan lokaci kafin ya rage daraja a kasuwar yan wasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.