fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Haaland ya zamo dan wasan firimiya na farko dayaci kwallaye a wasannin waje hudu daya fara bugawa

Tauraron dan wasan gaba na kungiyar Manchester City, Erling Haaland na cigaba da haskakawa a gasar firimiya ta kasar Ingila.

Inda ya sake taimakawa kungiyar a wasanta na yau ta lallasa Wolves daci uku bako daya bayan Jack Grealish, kuma Foden sun ci mata kwallaye biyu.

Kwallon da Haaland yaci tasa ya zamo dan wasa na farko a tarihin gasar firimiya dayaci kwallaye a wasannin waje guda hudu daya fara bugawa.

Yayin da kuma kwallon ta kasance ta 100 daya ci a wasanni 99 da suka gabata daya buga tun shekarar 2020, sakamakon wasan yasa City ta dare saman teburin firimiya da maki 17 inda ta wuce Arsenal da maki biyu.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.