fbpx
Thursday, May 26
Shadow

“(Haba dai) Kalli sauran matan da kuka dauki hoto tare mana: Ke kadaice gashin kanki a waje”>>Wasu suka jawo hankalin Rahama Sadau

Hankalin wasu mutane yakai kan wannan hoton da korarriyar, fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta dauka tare da wasu masoyanta da suka tayata murnar zagayowar ranar haihuwarta acan kasar Cyprus, wadanda suka yi magana akan wannan hoton sunyi kira da cewa ya kamata Rahamar ta lura da sauran matan da suke tare da ita a wannan hoton duk sun rufe kawunansu amma ita kadaice gashinta a waje.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wani cewa yayi “Ina tayaki murnar zagayowar ranar haihuwarki, an dade ba’a haduba, amma da kin rufe gashin kanki(zaifi), duba fa kiga duk sauran abokanki mata(da kuka dauki hoton tare dasu) sun rufe gashin kawunansu”.

Wani kuwa cewa yayi “ba wai zanyi suka a gareki bane, Amma me zai hana ki rufe kanki mana? Wallahi tallahi ina mugun sonki kuma ina baki uzuri matuka, in takaice miki zance, wannan ne karo na farko da naga laifinki……Dan Allah ki kiyaye, ki nuna musu cewa ke musulmace. Akalladai a rufe kai”


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Fasto Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Da ‘Yan Tawayen IPOB Suka Yi Wa Fatima Da ‘Ya’yanta Hudu A Jihar Anambara

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.