Hadakar hukumar ‘yan sanda tayi nasarar ceto wani dan kasar sin daya tare da wasu mutane biyu a hannun masu garkuwa da mutane a Kaduna.
Mai magana da yawun hukumar na jihar ne ya bayyana hakan, Muhammad Jalinge wanda yace hadakar hukumar sunyi nasarar ceto su ne a kauyen Sabon Sara a hanyar Abuja.
Inda yace sunyi musayar wuta da ‘yan bindigar ne a karshe suka tsere har suka bar mashinan su guda takwas, kuma da misalin karfe daya na dare ne suka kai masu harin.