Hadakar jamj’an tsaro sunyi nasarar kashe ‘yan bindiga 10 a jihar Niger bayan da ‘yan bindigar sukayi yunkurin hana shagulgulan Sallah a karamar hukumar Rafi.
Kwamishinan kananun hukumomi kuma shugaban tsaro na jihar, Emmanuel Umar ne ya tabbatar da hakan a ranar talata.
Hadakar jami’an tsaron sunyi nasarar ceto mutane 14 dake hannun ‘yan bindigar tare da babura bakwai.
Hare haren da ake kaiwa wasu bangarori a jihar Niger yayi kamari sosai, wanda hakan yasa har mutane sukafara hijira.