fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Hadarin mota a Kano ya yi sanadiyyar mutum biyu, yayin da mutane biyar suka jikkata

An tabbatar da mutuwar mutum biyu yayin da wasu biyar suka jikkata a wani hatsarin mota a kan hanyar Kano zuwa Zariya da ke kauyen Dakatsalle.
Kwamandan sashin na FRSC a jihar Kano, Mista Zubairu Mato, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, NAN ta ruwaito.
Mato ya ce hatsarin ya rutsa da motar kirar Peugeot 306 mai lamba TFA 429 TJ da tirela mai lamba KTJ 574 XA.
“Mun samu kiran waya da misalin karfe 3:15 na safiyar ranar 29 ga Maris, 2021.
“Da samun wannan bayanin, muka hanzarta tura jami’ai da motocinmu zuwa wurin da abin ya faru domin ceton wadanda abin ya shafa da karfe 3:40 na safe.”
Kwamandan sashen ya kara da cewa hatsarin ya afku ne sakamakon saurin gudu da kuma rashin kulawa.
“Hatsarin ya rutsa da manya maza 13. Wadanda abin ya rutsa da su, an rasa rayukankan maza biyu ne manya, yayin da maza biyar da abin ya shafa suka samu munanan raunuka, ”ya kara da cewa.
Ya ce an kai wadanda suka jikkata babban asibitin Kura don kulawa, yayin da gawarwakin mamatan ’yan sanda suka mika su ga danginsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Bidiyo: ISWAP ta ɗauki nauyin kai hari gidan yarin Kuje

Leave a Reply

Your email address will not be published.