fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hadarin Mota ya ci rayukan mutane 17 a hanyar Abuja

Mutane 17 ne suka rasa rayukansu a hadarin motar da ya faru a hanyar Abuja zuwa Lokoja, hadarin ya farune a daidai garin Irepene.

 

Hadarin ya farune a yau da misalin karfe 5 na yamma inda motocin Toyota Hiace da motar safa me daukar fasinjoji da yawa.

 

Mutane 15 ne suka mutu nan take. Bayan da aka kai wanda suka jikkata Asibiti, wasu karin 2 sun kara Mutuwa.

Kwamandan FRSC na jihar Kogi Solomon Agure ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yanda The Nation ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published.