Wani hatsarin mota da ya afku a babban hanyar Calaba a jihar Korus Ribas yayi sanadin salwantar rayukan mutum 9 tare da jikkata wasu mutum 3.
Kwamandan, Hukumar Kiyaye Haddura (FRSC) a jihar Kuros Riba Cyprian Ofordu ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya shaida cewa a kalla mutum 12 lamarin ya rusa dasu yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum 9 baya ga haka hukumar tayi Nasarar ceto mutane uku daga cikin wadanda lamarin ya rutsa dasu wadanda a yanzu haka suke cikin muyicin hali.
Jami’in hukumar ya bayyana cewa har zuwa yanzu hukumar bata gama tantance musabbabin da ya haddasa hadari ba.