fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 5, tare da jikkata wasu 9 a jihar Bauchi

Mutane 5 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a jihar Bauchi a ranar Laraba, kamar yadda hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta tabbatar a ranar Alhamis.

Kwamandan hukumar FRSC a jihar, Yusuf Abdullahi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa wasu mutane tara sun samu munanan raunuka a hadarin.

Ya ce hatsarin ya afku ne a unguwar Nabordo dake kan hanyar Toro zuwa Bauchi inda wasu motoci biyu suka yi karo da juna.

Abdullahi ya ce, cikin mintuna 26 hukumar FRSC ta isa wurin da hadarin ya afku domin share wurin.

A cewarsa, ba a samu lambobin rajistar motocin biyu ba, amma na kamfanonin sufurin Gombe Line da Adamawa Sunshine ne.

Ya kuma bayyana motocin a matsayin Toyota Hummer Bus da Toyota Sienna, kuma ya alakanta musabbabin hadarin da tuki mai hatsari da kuma keta gudu.

Karanta wannan  Ji bayani dalla-dalla yanda 'yan Bindiga suka kaiwa tawagar motocin shugaba Buhari hari

“Mutane 15 ne suka hada da maza 13 da mata biyu.

“Biyar sun mutu nan take kuma dukkansu maza ne. Wasu tara kuma sun samu raunuka, daga cikinsu akwai maza takwas da mace daya; Mutum daya tilo da ya tsira ba tare da wani rauni ba, mace ce,” Abdullahi ya ce.

Abdullahi ya ce an kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Toro domin yi musu magani.

Abdullahi ya kuma bukaci masu ababen hawa da su tabbatar da cewa motocinsu na cikin koshin lafiya kafin su fara tafiye-tafiye.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.