fbpx
Friday, July 1
Shadow

Hadarin mota yayi sanadiyyar mutuwar mutane 18 akan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Wani mummunan hadarin mota yayi sanadiyyar mutuwar mutane 18 akan hanyar Kaduna zuwa Abuja a yau, Talata.

 

Lamarin ya faru a daidai garin Katari kamar yanda Leadership ta ruwaito.

Wani shaida ya gayawa Leadership din cewa motar bas ce dake dauke da mutane 18 ta yi karo da babbar mota dake ajiye a kan titi ba tare da saka wata alama ba.

 

Yace duka mutanen dake cikin motar sun mutu, hukumar kiyaye hadura, reshen jihar sun tabbatar da faruwar lamarin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.