Kakakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Femi Adesina ya bayyana cewa, hadiman shugaban kasar suma mutanene kamar kowa, saboda haka dan cutar coronavirus ta kamasu ba abin mamaki bane.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV.
Yace lallai sun kamu amma hakan ba abin mamaki bane dan suma mutanene kamar kowa.
Saidai yace cutar bata yi tsanani a jikinsu ba.