Hadimin gwamnan Jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai ya caccaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan rikicin Hausawa da Yarbawa a Oyo.
A yace rubutun da shugaban kasar yayi a shafukan sada zumunta sun yi kadan su magance matsalar.
Yace ya kamata shugaban kasar ya dauki mataki da gaggawa kamin lokaci ya kure.
A baya dai Gwamnan Kano ya taba dakatar da Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Rikicin Hausawa da Yarbawa a Oyo ya dauki hankula sosai inda ya saka fargaba a garin.
“@MBuhari your 2 tweets arent enough to end this barbarism,” Yakasai tweeted with his verified Twitter handle @Dawisu on Monday.
“Take action, & take action NOW b4 its too late,” he added., Guardian.