Mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa shugaba Buhari ya bar Najeriya zuwa kasar Ingila 9 ga watan Afrilu.
Rahotanni sun yi ta yaduwa a yanar gizo a yau cewa shugaban ya bar kasar domin hutun kwanaki 20 a kasar Birtaniya.
Da yake karyata labarin a shafinsa na Twitter, Bashir ya rubuta;
‘Labarin da ke yawo cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi hutun kwanaki 20 zuwa Landan karya ne. Shugaban kasa yana Abuja kuma ba ya shirin yin wata tafiya zuwa Landan.”