A ranar Alhamis din da ta gabata ne, hukumar kiyaye haddura reshan jihar Ogun (TRACE), ta sanar da cewa, a kalla mutum 109 ne suka rasa rayukansu a hadurra da suka faru a fadin jihar Ogun tsakanin watan Janairu zuwa watan Agusta.
Kwamandan rundunar Mista Seeni Ogunyemi ne ya bayyana hakan a wajen taron kwamandojin rundunar TRACE Corps na shekara-shekara karo na 5, wanda aka gudanar a Valley View, dake Abeokuta.
Ya zargi cewa, gudun wuce sa”a da tuki cikin rashin bin doka sune ummul-aba’isin da su ke haifar da yawan hadarurruka akan hanyoyi wanda suke janyo mace-mace a jihar.
A cewarsa, a kalla mutane 450 ne suka samu raunuka a hadurru mota daban-daban da su ka afku a tsakanin lokutan.
Hakanan kwamandan rundunar ya yabawa gwamnatin jihar bisa gudunmawar da take bawa hukumar na kayayyakin aiki domin cigaba da gudanar ta ayyukanata cikin Nasar.