Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da hafsoshin tsaro a babban birnin tarayya yau ranar alhamis kan matsalar tsaro.
Hafsoshin tsaron sun bayyana masa cewa kwanan nan zasu kawo karshen ‘yan bindiga da kuma matsalar tsaro a kasar bakidaya.
Sannan sun gargadi manema labarai cewa su daina yada ko wani irin labarai kan matsalar tsaro domin hakan na karawa ‘yan bindiga karfi.
Buhari ya gana dasu ne bayan sanatoci sun bayyana cewa zasu tsige shi, sannan kuma suma ‘yan bindiga sunce zasu yi garkuwa dashi.