Saturday, July 13
Shadow

Hajji 2024: Fiye da maniyyata miliyan ɗaya da rabi ne za su sauke farali

Hukumomin Saudiyya sun ce fiye da mutum miliyan ɗaya da rabi ne suka isa ƙasar, daga sassan duniya daban-daban domin gudanar da akin hajjin bana.

Jaridar Saudi Gazzet, ta ruwaito babban daraktan ofishin kula da bayar da biza na ƙasar, na cewa maniyyata miliyan 1,547,295 ne suka isa ƙasar ta sama da kan iyakokin ƙasa da kuma tasoshin jiragen ruwa.

Ya ƙara da cewa maniyyata miliyan 1,483,312 ne suka shiga ƙasar ta jiragen sama, yayin dan mutum 59,273 suka shiga ƙasar ta kan iyakokin ƙasa, sai kuma maniyyata 4,710 da suka je ta jiragen ruwa.

A ranar Juma’a 8 ga watan Dhul-Hijja ne za a fara gudanar da aikin Hajji na wannan shekarar.

Karanta Wannan  Yau ake kammala aiki Hajji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *