fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Hakeem Baba Ahmad ya yabawa Elrufai bisa jawabin da yawa ‘yan Kaduna saidai yace akwai bukatar jawabin dalilin bude gari amma a hana yin Sallah

Jigo a jihar Kaduna, Hakeem Baba Ahmad ya yabawa gwamna Nasiru Ahmad El-Rufai kan jawabin da ya yiwa mutanen jihar kan dokar zaman gida inda yace yayi abinda ya kamata.

 

Saidai yace akwai bukatar fayyacewa mutane dalilin bude gari na tsawon kwanaki 2 a sati amma kuma a hana yin Sallah.

 

Ga jawabinshi na Facebook kamar haka:

 

‘Jawabin da Gwamna Nasir el-Rufai da mai dakinsa suka yi wa jama’ar Jihar Kaduna a kan muhimmancin bin dokoki da tsare kai da ban hakuri ya cancanta. Wajibine shugabanni su rika bayyana wa talakawa matakan da suka dauka,kuma su nuna tausayi da damuwar su idan matakan da suka dauka sun kuntata wa jama’a.Haka kuma fitowa da yayi da kan sa, ba sako ba, yana da kyau domin komin girma shugaba bai wuce yayi wa jama’a magana shi da su ba.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Sai dai Gwamna sai ya kara damarar yi wa jama’a Musulmi bayani a kan hana su zuwa Sallar Idi idan wannan shi zai zama matsayin gwamnatin sa.

 

Jama’a zasu hura wuta a bayyana masu hujjar sakin gari har na kwana biyu a mako,amma a hana su zuwa Sallar Idi ta awa daya.Wadannan matsaloli na Sallar Idi da Jumma’a da yadda ake raba tallafi su na da muhimmanci, kuma ya kamata Gwamna ya mai da hankali da kan sa wajen fayyace inda gwamnatin sa ta sa gaba a game da su da hujjojin ta.

 

Allah Ya bamu ladan ibada,Ya tsare mu da tsarewar Sa.’

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.