Jam’iyyar APC me mulki tace hakurin da jigonta kuma me neman tikitin ta na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar kan shugaban kasa, Muhammadu Buhari bayan yayi masa gori bai isa ba.
Shugaban jam’iyyar, Abdullahi Adamu ne ya bayyana haka inda yace akwai yiyuwar su hukunta Bola Ahmad Tinubu.
Tinubu dai a yayin da yake magana da yarbanci a wajan wani taron siyasa, yace shine yayi silar zaman shugaban kasa, Muhammadu Buhari shugaban kasa, amma yanzu shugaban kasar na neman jiya masa baya.
Wannan kalamai na Tinubu dai sun jawo Allah wadai da cece-kuce sosai.