fbpx
Sunday, December 4
Shadow

“Halayen wannan abokiyar tawa sukasa na shiga addinin musulunci”>>inji inyamura data musulunta, A’ishat Obi

A kwanakin bayane wata Inyamura me suna A’ishat Obi data amshi addinin musulunci ta fito ta bayyanawa ‘yan uwanta Inyamurai da Duniya cewa addinin na musulunci ya samu kafuwa a yankin Inyamuran kuma tana kira ga ‘yan uwanta da suka amshi musulunci dasu tashi tsaye su nemi ilimin addinin.

A yau kuma A’isha, wadda ke sanye da hijabi a wannan hoton na sama ta bayyana abokiyarta, me sanye da gyale, cewa tana daya daga cikin mutanen da kyawawan halayensu ya jawo hankalinta zuwa shiga addinin na musulunci.

A’isha ta kara da cewa wannan ‘yar uwatace, kai tamafi karfin ‘yar uwa a gareni domin tana daga cikin wadanda kyawawan halayyarsu ya jani na amshi addinin musulunci, kuma ina fatan gamuwa da ita idan Allah ya tashemu kiyama,  A’isha tayi fatan cewa Allah ya bata ikon amfanar da mutane itama.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Shaykh mufti Ismail Menk taréda Farfesa Isa Alí Ibrahim (Pantami) a wajén taron zaman lafìya da hadin kai na dunìya 2022 da ké gudana yanzu haka a bírnín tarayya Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *