fbpx
Thursday, July 2
Shadow

Halin da ake ciki kan Coronavirus/COVID-19 a Najeriya

A halin da ake ciki a kan Annobarnan na Coronavirus/COVID-19 a Najeriya a takaice.

 

Mutanen dake dauke da cutar a Najeriya sun kai 51.

 

 

Gwamnonin Edo, dana Ondo da karamar ministar Abuja sun killace kansu kan cutar Coronavirus/COVID-19 suna jiran sakamakon gwajin da aka musu.

 

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello yace bashi da cutar Coronavirus/COVID-19 kuma duk masu mai fata in Allah ya yarda sai ciwom Kanjamau ya kamasu.

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa,  Atiku Abubakar ya baiwa gwamnati tallafin Miliyan 50 dan yakar Coronavirus/COVID-19 inda yayi kira da a tausayawa talakawa.

 

Gwamnatin Kano ta bayar da sanarwar rufe jihar, ba shiga ba fita sannan a rufe guraren tarukan jama’a.

 

Shugaba Buhari a jiya,Laraba ya koma bakin aiki bayan killace kansa.

 

Jaridun Punch, Thisday, Guardian, Vanguard, na daga cikin jaridun da gwamnatin taryya ta dakatar daga kawo Rahoto daga fadar shugaban kasa inda ta bar jaridu 13.

 

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *