Kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta nuna bacin ranta kan matakin da kungiyar IPOB ta dauka na hana kai shanu kudu.
ACG tace hakan matakine na takala da kuma neman yaki.
Kakakin ACF, Emmanuel Yawe ne ya bayyana haka inda yace sam wannan mataki bai dace.
Kungiyar masu kai shanun kudu ta bayyana cewa tana shirin daina kai shanun, amma kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta yi kiran a zauna Lafiya.
Hakanan kungiyar ta kuma ce masu kai shanun kudu kada su daina, su yi watsi da barazanat ta IPOB.
IpOB dai dake son kafa kasar Biafra ta rika kona motocin dake hawa titi a yayin da ta rika saka dokar zaman gida dole.