Rahotanni daga bangaren Tinubu na cewa, hankalin mutanensa ya tashi sosai bayan da shugaban kwamitin da suka tantance ‘yan takarar shugaban kasa, John Oyegun ya bayyana cewa, matasan ‘yan takara kadai aka tantance.
Akwai dai mutane 10 da ba’a tantance ba wanda aka ce bau cancanci yima APC takarar shugabancin ba.
Jimullar ‘yan takara 23 ne APC ta tantance.
Oyegun ya bayyana hakane yayin mika rahotonsu ga shugaban APC, Abdullahi Adamu a yau Juma’a.