fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Hankulan matafiya sun matukar tashi yayin da ‘yan bindiga suka kaiwa rundunar soji harin kwantan bauna akan babbar hanyar Kaduna zuwa babban birnin tarayya

Hankulan matafiya sun matukat tashi bayan da ‘yan bindiga suka kaiwa rundunar soji harin kwantan bauna a babban birnin tarayya Abuja.

A daren jiya ne wannan iftila’in ya faru a akan babbar hanyar Kaduna zuwa babban birnin tarayyar wato Abuja daidai Madalla junction.

Inda har aka samu rahoto cewa ‘yan bindigar sun kashe wasu daga cikin rundunar sojin kafin suka tsere suka koma cikin daji.

Matafiya da dama sun ki gaba sunki baya sun tsaya a wuri guda hankula sun tashi inda har wani daga cikinsu yayi bideyo yana neman agaji.

Leave a Reply

Your email address will not be published.